>

Abubakar Mahmoud Gumi — 66

3:122 A lõkacin da ƙungiyõyi[1] biyu daga gare ku suka yi niyyar su karye, kuma Allah ne Majiɓincinsu, don haka, ga Allah mũminai sai su dogara.

3:123 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a Badar, alhãli kuwa kunã mafiya rauni, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, kuna gõdẽwa.

3:124 A lõkacin da kake cẽwa ga mũminai, "Shin bai ishe ku ba, Ubangijinku Ya taimake ku da dubu uku daga malã'iku saukakku?"

3:125 "Na'am! Idan kuka yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, kuma suka zo muku da gaugawarsu, irin wannan, Ubangijinku zai ƙãre ku da dubu biyar daga malãiku mãsu alãma."

3:126 Kuma Allah bai sanya shi[1] ba, fãce dõmin bushãra a gare ku, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi. Taimako bai kasance ba fãce daga wurin Allah, Mabuwãyi, Mai hikima.

3:127 Dõmin Ya katse wani gẽfe daga waɗanda suka kãfirta ko kuma Ya ƙasƙantã su, har su jũya, suna mãsu ruɓushi.

3:128 Bãbu kõme a gare ka game da al'amarin (shiryar da su banda iyar da manzanci). Ko Allah Ya karɓi tũbarsu, kõ kuwa Ya yimusu azãba, to lalle ne sũ, mãsu zãlunci ne.

3:129 Allah ne da mulkin abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, yana gãfarta wa wanda Yake so, kuma yana azabta wanda Yake so, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

3:130 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci riba ninkininki, riɓanye, kuma ku bi Allah da taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara.

3:131 Kuma ku ji tsõron wutã wadda aka yi tattali dõmin kãfirai.

3:132 Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, tsammaninku a yi muku rahama.