Abubakar Mahmoud Gumi — 604
112:1 "Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci."
112:2 "Allah wanda ake nufin Sa da buƙata."
112:3 "Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba."
112:4 "Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi
113:1 "Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya"
113:2 "Daga sharrin abin da Ya halitta."
113:3 "Da sharrin dare, idan ya yi duhu."
113:4 "Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin kuduri"
113:5 "Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada."
114:1 "Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."
114:2 "Mamallakin mutane."
114:3 "Abin bautãwar mutãne."
114:4 "Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa."[1]
114:5 "Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane."
114:6 "Daga aljannu da mutane."