Abubakar Mahmoud Gumi — 603
109:1 Ka ce: "Ya kũ kãfirai!"
109:2 "Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba."
109:3 "Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba."
109:4 "Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba."
109:5 "Kuma kũ, ba ku zama mãsu bautã wa abin da nake[1] bautã wa ba."
109:6 "Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni."
110:1 Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara.
110:2 Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, ƙungiya-ƙungiya.
110:3 To, ka yi tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karɓar tũba ne.
111:1 Hannãye biyu na Abũlahabi sun halaka, kuma ya halaka.
111:2 Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra.
111:3 Zã ya shiga wuta mai hũruwa.
111:4 Tãre da matarsa mai ɗaukar itacen (wuta).[1]
111:5 A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ¡iyãma).