Abubakar Mahmoud Gumi — 601
103:1 Ina rantsuwa da zãmani.[1]
103:2 Lalle ne mutum yana a cikin hasara.
103:3 Fãce waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri (su kam, basu cikin hasara).
104:1 Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).
104:2 Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.
104:3 Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.
104:4 A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.
104:5 Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?
104:6 Wutar Allah ce wadda ake hurawa.
104:7 Wadda take lẽƙãwa a kan zukata.
104:8 Lalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu.
104:9 A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.
105:1 Ashe, ba ka ga yadda Ubangijin ka Ya aikata ga mutanen giwa[1] ba?
105:2 Ashe, bai sanya kaidin su a cikin ɓata ba?
105:3 Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.
105:4 Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
105:5 Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?