>

Abubakar Mahmoud Gumi — 600

100:6 Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.

100:7 Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka.

100:8 Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.

100:9 Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.

100:10 Aka bayyana abin da ke cikin zukata.

100:11 Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?

101:1 Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!

101:2 Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?

101:3 Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?

101:4 Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.

101:5 Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.

101:6 To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.

101:7 To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.

101:8 Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).

101:9 To, uwarsa Hãwiya ce.

101:10 Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?

101:11 Wata wuta ce mai kuna.

102:1 Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (daga ibada mai amfaninku).

102:2 Har kuka ziyarci kaburbura.

102:3 A'aha! (Nan gaba) zã ku sani.

102:4 Sa'an nan, tabbas, zã ku sani.

102:5 Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.

102:6 Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.

102:7 Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.

102:8 Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku).