>

Abubakar Mahmoud Gumi — 6

2:30 Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya ce ga malã'iku: "Lalle ne, Ni Mai sanya wani halĩfa ne a cikin ƙasa," suka ce: "Ashe, zã Ka sanya a cikinta, wanda zai yi ɓarna a cikinta, kuma mu, muna yi maka tasbihi tare da gõde maka, kuma[1] muna tsarkakewa gareka" Ya ce: "Lalle ne, Ni Na san abin da ba ku sani ba."

2:31 Kuma Ya sanar da Ãdam sũnãye dukansu, sa'an nan kuma ya gitta su a kan malã'iku, sa'n nan Ya ce: "Ku gaya mini sũnayen waɗannan, idan kun nasance mãsu gaskiya."

2:32 Suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka! Bãbu sani a gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Masani, Mai hikima."

2:33 Ya ce: "Yã Ãdam! Ka gaya musu sũnãyensu." To, a lokacin da ya gaya musu sũnãyensu, (Allah) Ya ce: "Ashe, ban ce muku [1]ba, lalle Ni, Inã sane da gaibin sammai da ƙasa, kuma (Inã sane da) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓõyewa?"

2:34 Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam," Sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa ya ƙi, kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.

2:35 Kuma muka ce: "Ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna, kuma ku ci daga gare ta, bisa wadãta, inda kuke so, kuma kada ku kusanci wannan itãciyar, har ku kasance daga azzãlumai."

2:36 Sai Shaiɗan ya talãlãɓantar da su ga barinta, sai ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa. Kuma muka ce: "Sãshenku nã maƙiyi ga sãshe, kuma kuna da a cikin ƙasa matabbata da jin dãɗi zuwa ga wani lõkaci."

2:37 Sai Ãdam ya karɓi wasu kalmõmi daga Ubangjjinsa, sabõda haka ya karɓi tũba a kansa. Lalle ne Shi, Shĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.