Abubakar Mahmoud Gumi — 597
94:3 Wanda ya nauyayi bãyanka?
94:4 Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
94:5 To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
94:6 Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
94:7 Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).
94:8 Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.
95:1 Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.[1]
95:2 Da Dũr Sĩnĩna.[1]
95:3 Da wannan gari[1] amintacce.
95:4 Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
95:5 Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
95:6 Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
95:7 To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
95:8 Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?[1]
96:1 Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.
96:2 Ya hahitta mutum daga gudan jini.
96:3 Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci.
96:4 Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.
96:5 Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.
96:6 A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).
96:7 Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.
96:8 Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.
96:9 Shin, kã ga wanda ke hana.
96:10 Bãwã idan yã yi salla?
96:11 Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?
96:12 Ko ya yi umurni da taƙawa?