>

Abubakar Mahmoud Gumi — 595

90:19 Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Mu, sũ ne ma'abũta shu'umci[1]

90:20 A kansu akwai wata wuta abar kullewa.

91:1 Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.

91:2 Kuma da wata idan ya bi ta.

91:3 Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.

91:4 Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.

91:5 Da sama da abin da ya gina ta.

91:6 Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.

91:7 Da rai da abin da ya daidaita shi.

91:8 Sa'an nan ya yi masa Ilhamar fãjircinsa da shiryuwarsa.

91:9 Lalle ne wanda ya tsarkake[1] shi (rai) ya sãmi babban rabo.

91:10 Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe[1] shi (da laifi) ya tãɓe.

91:11 Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.

91:12 A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).

91:13 Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"

91:14 Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).

91:15 Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).

92:1 Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.

92:2 Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.

92:3 Da abin da ya halitta namiji da mace.

92:4 Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.

92:5 To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.

92:6 Kuma ya gaskata kalma[1] mai kyãwo.

92:7 To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.

92:8 Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.

92:9 Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.