>

Abubakar Mahmoud Gumi — 593

88:23 Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.

88:24 To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.

88:25 Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.

88:26 Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.

89:1 Inã rantsuwa da alfijiri.

89:2 Da darũruwa gõma.

89:3 Da (adadi na) cikã da (na) mãrã.

89:4 Da dare idan yana shũɗewa.

89:5 Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?

89:6 Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?

89:7 Iramawa mãsu sakon[1] ƙĩrar jiki.

89:8 Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya).

89:9 Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi[1] suka yi gidãje)?

89:10 Da Fir'auna mai turãku.

89:11 Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?

89:12 Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.

89:13 Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.

89:14 Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.

89:15 To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni."

89:16 Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni."

89:17 A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!

89:18 Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!

89:19 Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.

89:20 Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa.

89:21 A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.

89:22 Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, sahu- sahu.