>

Abubakar Mahmoud Gumi — 592

87:11 Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,

87:12 Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.

87:13 Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.

87:14 Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.

87:15 Kuma ya ambaci sũnan[1] Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.

87:16 Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.[1]

87:17 Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.

87:18 Lalle ne, wannan[1] yanã a cikin littafan farko.

87:19 Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.

88:1 Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?

88:2 Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.

88:3 Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.

88:4 Zã su shiga wata wuta mai zãfi.

88:5 Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.

88:6 Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.

88:7 Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.

88:8 Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.

88:9 Game da aikinsu, masu yarda ne.

88:10 (Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.

88:11 Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.

88:12 A cikinta akwai marmaro mai gudãna.

88:13 A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.

88:14 Da kõfuna ar'aje.

88:15 Da filõli[1] jẽre,

88:16 Da katifu shimfiɗe.

88:17 Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?

88:18 Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?

88:19 Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?

88:20 Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?

88:21 sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.

88:22 Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.