Abubakar Mahmoud Gumi — 591
86:1 Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
86:2 To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
86:3 Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.[1]
86:4 Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
86:5 To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
86:6 An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
86:7 Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
86:8 Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
86:9 Rãnar da ake jarrabawar asirai.
86:10 Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
86:11 Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
86:12 Da ƙasa ma'abociyar tsãgẽwa,[1]
86:13 Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki[1]
86:14 Kuma shĩ bã bananci[1] bane
86:15 Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
86:16 Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
86:17 Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.
87:1 Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
87:2 Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
87:3 Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
87:4 Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
87:5 Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
87:6 Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
87:7 Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
87:8 Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.
87:9 Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
87:10 Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.