>

Abubakar Mahmoud Gumi — 589

83:34 To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.

83:35 A kan karagu, suna ta kallo.

83:36 Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?[1]

84:1 Idan sama ta kẽce,

84:2 Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron,

84:3 Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta,

84:4 Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme.

84:5 Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren,

84:6 Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne.

84:7 To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa.

84:8 To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi.

84:9 Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha.

84:10 Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa.

84:11 To, zã shi dinga kiran halaka!

84:12 Kuma ya shiga sa'ĩr.

84:13 Lale ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha.

84:14 Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba.

84:15 Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.

84:16 To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba.

84:17 Da dare, da abin da ya ƙunsa.

84:18 Da watã idan (haskensa) ya cika.

84:19 Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli.

84:20 To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni?

84:21 Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u?

84:22 Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi.

84:23 Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa.

84:24 Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.