>

Abubakar Mahmoud Gumi — 587

82:1 Idan sama ta tsãge.

82:2 Kuma idan taurãri suka wãtse.

82:3 Kuma idan tẽkuna aka facce su.

82:4 Kuma idan kaburbura aka tõne su.

82:5 Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.

82:6 Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci.

82:7 Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.

82:8 A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.

82:9 A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!

82:10 Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.

82:11 Mãsu daraja, marubũta.

82:12 Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.

82:13 Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.

82:14 Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.

82:15 Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.

82:16 Bã zã su faku daga gare ta ba.

82:17 Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa ranar sakamako?

82:18 Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?

82:19 Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.

83:1 Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.

83:2 Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.

83:3 Kuma idan sun auna musu da zakka[1] ko da sikẽli, suna ragẽwa

83:4 Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?