>

Abubakar Mahmoud Gumi — 586

80:41 Baƙi zai rufe su.

80:42 Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).

81:1 Idan rãna aka shafe haskenta

81:2 Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).

81:3 Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.

81:4 Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna[1] aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.

81:5 Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.

81:6 Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.

81:7 Kuma idan rãyuka aka haɗa[1] su da jikunkunansu.

81:8 Kuma idan wadda aka turbuɗe[1] ta da rai aka tambaye ta.

81:9 "Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"

81:10 Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).

81:11 Kuma idan sama aka fẽɗe ta.

81:12 Kuma idan Jahĩm aka hũra ta

81:13 Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.

81:14 Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).

81:15 To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã[1] ba.

81:16 Mãsu gudu suna ɓũya.

81:17 Da dare idan ya bãyar da bãya.

81:18 Da sãfiya idan ta yi lumfashi.

81:19 Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.

81:20 Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.

81:21 Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.

81:22 Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.

81:23 Kuma lalle ne, yã gan shi[1] a cikin sararin sama mabayyani.

81:24 Kuma shi, ga gaibi[1] bã mai rowa ba ne.

81:25 Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.

81:26 Shin, a inã zã ku tafi?

81:27 Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.

81:28 Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.

81:29 Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.