>

Abubakar Mahmoud Gumi — 583

78:31 Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.

78:32 Lambuna da inabõbi.

78:33 Da yan Mata tsaraikun Juna

78:34 Da hinjãlan giya cikakku.

78:35 Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.

78:36 Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.

78:37 Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.

78:38 Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.

78:39 Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.

78:40 Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"

79:1 Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.

79:2 Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.

79:3 Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.

79:4 Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umarnin Allah) kamar suna tsẽre.

79:5 Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni.

79:6 Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.

79:7 Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.

79:8 Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.

79:9 Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.

79:10 Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?

79:11 "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"

79:12 Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"

79:13 To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.

79:14 Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.

79:15 Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?

79:16 A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?