>

Abubakar Mahmoud Gumi — 582

78:1 A kan mẽ suke tambayar jũna?

78:2 A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?

78:3 Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?

78:4 A'aha! Zã su sani.

78:5 Kuma, a'aha! Zã su sani.

78:6 Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?

78:7 Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?

78:8 Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?

78:9 Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?

78:10 Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?

78:11 Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?

78:12 Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?

78:13 Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?

78:14 Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?

78:15 Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?

78:16 Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?

78:17 Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.

78:18 Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.

78:19 Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.

78:20 Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.

78:21 Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.

78:22 Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.

78:23 Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.

78:24 Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.

78:25 Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.

78:26 Sakamako mai dãcẽwa.

78:27 Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.

78:28 Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, ƙaryatãwa!

78:29 Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.

78:30 Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.