Abubakar Mahmoud Gumi — 580
76:26 Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo.
76:27 Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi.
76:28 Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa.
76:29 Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa.
76:30 Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima.
76:31 Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.
77:1 Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
77:2 Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
77:3 Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
77:4 sa'an nan, da ãyõyi[1] mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
77:5 Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
77:6 Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
77:7 Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
77:8 To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
77:9 Kuma, idan sama aka tsãge ta.
77:10 Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
77:11 Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
77:12 Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
77:13 Domin rãnar rarrabẽwa.[1]
77:14 Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
77:15 Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
77:16 Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
77:17 Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
77:18 Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
77:19 Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!