>

Abubakar Mahmoud Gumi — 578

75:20 A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.

75:21 Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).

75:22 Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.

75:23 Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.

75:24 Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.

75:25 Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.

75:26 A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.

75:27 kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"

75:28 Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.

75:29 Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.

75:30 Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa[1] take.

75:31 To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!

75:32 Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!

75:33 Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.

75:34 Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.

75:35 Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.

75:36 Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?

75:37 Bai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)

75:38 Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;

75:39 Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?

75:40 Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?[1]

76:1 Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata.

76:2 Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani,

76:3 Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci.

76:4 Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr.

76:5 Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne.