>

Abubakar Mahmoud Gumi — 577

74:48 Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba.

74:49 Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya.

74:50 Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne.

74:51 Sun gudu daga zãki.

74:52 A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa

74:53 A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira.

74:54 A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce.

74:55 Dõmin wanda ya so, ya tuna.

74:56 Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara.

75:1 Bã sai Nã yi rantsuwa[1] da Rãnar ¡iyãma ba.

75:2 Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin[1] kansa ba.

75:3 Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?

75:4 Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.

75:5 Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.

75:6 Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"

75:7 To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).

75:8 Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).

75:9 Aka tãra rãnã da watã

75:10 Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"

75:11 A'aha! bãbu mafaka.

75:12 zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.

75:13 Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.

75:14 Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.

75:15 Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).

75:16 Kada ka mõtsar[1] da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).

75:17 Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.

75:18 To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.

75:19 sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.