>

Abubakar Mahmoud Gumi — 574

73:1 Yã wanda ya lulluɓe!

73:2 Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan.

73:3 Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi.

73:4 Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki.

73:5 Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi.

73:6 Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana.

73:7 Lalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo.

73:8 Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa gare Shi, yankewa.

73:9 Shi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda haka ka riƙe Shi wakili.

73:10 Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai kyãwo.

73:11 Kuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan.

73:12 Lalle ne, a wurin Mu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm.

73:13 Da wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi.

73:14 Rãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai malãlã.

73:15 Lalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo[1] mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo[2] zuwaga Fir'auna,

73:16 Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani.

73:17 To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra (tsofaffi) mãsu hurhura.

73:18 Sama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa.

73:19 Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa.