Abubakar Mahmoud Gumi — 573
72:14 "Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa."
72:15 "Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama."
72:16 "Kuma dã sun tsayu[1] sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa."
72:17 "Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa."
72:18 "Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu)."
72:19 "Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah[1] ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa."
72:20 Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba."
72:21 Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri."
72:22 Ka ce: "Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun mafaka ba daga gare Shi."
72:23 "Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da Manzon Sa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har abada."
72:24 Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi.
72:25 Ka ce: "Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya masa dõgon ajali!"
72:26 "Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinsa ga kowa."
72:27 "Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya[1] gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi."
72:28 "Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga."