Abubakar Mahmoud Gumi — 565
68:17 Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.
68:18 Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa.
68:19 Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci.
68:20 Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare.
68:21 Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci.
68:22 Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa.
68:23 Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa).
68:24 "Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!"
68:25 Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu.
68:26 Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!"
68:27 "Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne."
68:28 Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?"
68:29 Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai."
68:30 Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu.
68:31 Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka."
68:32 "Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne."
68:33 Haka dai azãbar[1] take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã.
68:34 Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima.
68:35 Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi?
68:36 Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)?
68:37 Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?
68:38 Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa?
68:39 Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kan Mu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?
68:40 Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)?
68:41 Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya.
68:42 Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujada, sai bã zã su iyãwa ba.