>

Abubakar Mahmoud Gumi — 561

66:8 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kõma zuwa ga Allah kõmawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyãgun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu a rãnar da Allah bã Ya kunyatar da Annabi [1]da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi. Haskensu yanã tafiya a gaba gare su da jihõhin dãmansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gãfara. Lalle Kai, a kan dukkan kõme, Yã kai Mai ikon yi ne."

66:9 Yã kai Annabi! Ka yãki kãfirai da munãfwkai. Kuma ka tsananta a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce, kuma tir da makoma, ita.

66:10 Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka kãfirta[1]: mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu, sun kasance a ƙarƙashin wasu bãyi biyu daga bãyin Mu sãlihai, sai suka yaudare su, sabõda haka ba su wadãtar musu da kõme daga Allah ba. Kuma aka ce: "Ku shiga, kũ biyu, wutã tãre da mãsu shiga."

66:11 Kuma Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka yi ĩmãni; matar Fir'auna,[1] sa'ad da ta ce "Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurin Ka a cikin Aljanna. Kuma Ka tsĩrar da ni daga Fir'auna da aikinsa. Kuma Ka tsĩrar da ni daga mutãnen nan azzãlumai."

66:12 Da Maryama[1] ɗiyar Imrãna wadda ta tsare farjinta, sai Muka hũra a cikinsa daga rũhinMu. Kuma ta gaskata game da ãyõyin Ubangijinta da Littattafan Sa alhãli kuwa ta kasance daga mãsu tawãli'u.