Abubakar Mahmoud Gumi — 539
57:12 Rãnar da zã ka ga mũminai maza da mũminai mãtã haskensu nã tafiya a gaba gare su, da kuma dãma gare su. (Anã ce musu) "Bushãrarku a yau, ita ce gidajen Aljanna." Ruwa na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Wannan, shĩ ne babban rabo mai girma.
57:13 Rãnar da munafikai maza da munãfikai mãtã ke cẽwa waɗanda suka yi ĩmãni: "Ku dũbẽ mu, mu yi makãmashi daga haskenku!" A ce (musu): "Ku kõma a bãyanku, dõmin ku nẽmo wani haske." Sai a danne a tsakãninsu da wani gãru yanã da wani ƙyaure, a cikinsa nan rahama take, kuma a bãyansa daga wajensa azaba take.
57:14 Sunã kiran su, "Ashe, bã tãre muke da ku ba?" Su ce: "Ĩ, amma kũ, kun fitini kanku, kuma kun yi jiran wata masĩfa, kuma kunyi shakka, kuma waɗansu gũrace-gũrace sun rũɗe ku, har umurnin Allah ya jẽ muku, kumamarũɗi ya rũɗe ku game da Allah."
57:15 "To, a yau bã zã a karɓi fansa daga gare ku ba. Kuma bã zã a karɓa daga waɗanda suka kãfirta ba. Makõmarku wutã ce, ita ce mai dacẽwa da ku, kuma makõmarku ɗin nan tã mũnana."
57:16 Shin, lõkaci bai yi ba ga wa ɗanda suka yi ĩmãnĩ[1] zukãtansu su yi tawãlu'i ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya? Kada su kasance kamar waɗanda aka bai wa littãfi a gabãnin haka, sai zãmani ya yi tsawo a kansu, sabõda haka zukãtansu suka ƙẽƙashe, kuma masu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.
57:17 Ku sani cẽwa Allah Yanã rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta.[1] Lalle Mun bayyanamuku ãyõyi da fatan zã ku yi hankali.
57:18 Lalle mãsu gaskatãwa maza da mãsu gaskatãwa mãtã, kuma suka ranta wa Allah rance mai kyau, anã riɓanya musu, kuma suna da wani sakamako na karimci.