Abubakar Mahmoud Gumi — 537
56:77 Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
56:78 A cikin wani littafi tsararre.
56:79 Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
56:80 Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
56:81 Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
56:82 Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
56:83 To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
56:84 Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
56:85 Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
56:86 To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
56:87 Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.[1]
56:88 To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
56:89 Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
56:90 Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
56:91 Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
56:92 Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
56:93 Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
56:94 Da ƙõnuwa da Jahĩm,
56:95 Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
56:96 Sabõda haka, ka tsarkake[1] sũnan Ubangijinka, Mai karimci.
57:1 Abin da ke cikin sammai da ƙasa yã yi tasbĩhi ga Allah. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
57:2 Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa: Yanã rãyarwa kuma Yanã kashẽwa, kuma Shĩ Mai ikon yi ne a kan kõme.
57:3 Shĩ ne Na farko, Na ƙarshe, Bayyananne, Bõyayye, kuma Shĩ Masani ne ga dukkan kõme.