>

Abubakar Mahmoud Gumi — 536

56:51 "Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"

56:52 "Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."

56:53 "Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."

56:54 "Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."

56:55 "Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."

56:56 Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.

56:57 Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?

56:58 Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?

56:59 Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?

56:60 Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa[1] ba,

56:61 A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.

56:62 Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?

56:63 Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?

56:64 Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?

56:65 Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.

56:66 (Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"

56:67 "Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"

56:68 Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?

56:69 Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?

56:70 Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?

56:71 Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?

56:72 Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?

56:73 Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.

56:74 Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.

56:75 To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.

56:76 Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.