>

Abubakar Mahmoud Gumi — 535

56:17 Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.

56:18 Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.

56:19 Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.

56:20 Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.

56:21 Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.

56:22 Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.

56:23 Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.

56:24 A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.

56:25 Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.

56:26 Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.

56:27 Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?

56:28 (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.

56:29 Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.

56:30 Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.

56:31 Da wani ruwa mai gudãna.

56:32 Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.

56:33 Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.

56:34 Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.

56:35 Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.

56:36 Sa'an nan Muka sanya su budurwai.

56:37 Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.

56:38 Ga mazõwa dãma.

56:39 Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.

56:40 Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.

56:41 Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?

56:42 Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.

56:43 Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.

56:44 Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.

56:45 Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.

56:46 Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.

56:47 Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"

56:48 "Shin, kuma da ubanninmu na farko?"

56:49 Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."

56:50 "Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."