>

Abubakar Mahmoud Gumi — 534

55:70 A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyawun hãlãye, mãsu kyaun halitta.

55:71 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

55:72 Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.

55:73 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

55:74 Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.

55:75 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

55:76 Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.

55:77 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

55:78 Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.

56:1 Idan mai aukuwa ta auku.

56:2 Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.

56:3 (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.

56:4 Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.

56:5 Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.

56:6 Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.

56:7 Kuma kun kasance nau'i uku.

56:8 Watau mazõwa dãma[1]. Mẽne ne mazõwa dãma?

56:9 Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?

56:10 Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,

56:11 Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.

56:12 A ckin Aljannar ni'ima.

56:13 Jama'a ne daga mutãnen farko.[1]

56:14 Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.

56:15 (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙu.

56:16 Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.