Abubakar Mahmoud Gumi — 531
54:50 Kuma umurnin Mu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.
54:51 Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?
54:52 Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.
54:53 Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.
54:54 Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.
54:55 A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.
55:1 (Allah) Mai rahama.
55:2 Yã sanar da Alƙur'ani.
55:3 Yã halitta mutum.
55:4 Yã sanar da shi bayãni (magana).
55:5 Rãnã da watã a kan lissãfi suke.
55:6 Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i.
55:7 Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli.
55:8 Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin.
55:9 Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin.
55:10 Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.
55:11 A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.
55:12 Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.
55:13 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku [1]kuke ƙaryatãwa?
55:14 Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko.
55:15 Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.
55:16 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
55:17 Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.
55:18 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?