>

Abubakar Mahmoud Gumi — 529

54:7 ¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.

54:8 Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!"

54:9 Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata Bawan Mu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.

54:10 Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako."

54:11 Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.

54:12 Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umarni da aka riga aka ƙaddara shi.

54:13 Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.

54:14 Tanã gudãna, a kan idãnun Mu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.

54:15 Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni

54:16 To, yãyã azãbã Ta take da gargaɗi Na?

54:17 Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

54:18 Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗi Na?

54:19 Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.

54:20 Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.

54:21 To, yãya azãbã Ta take da gargaɗi Na?

54:22 Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

54:23 Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.

54:24 Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.

54:25 "Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!"

54:26 Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?

54:27 Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar[1] ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.