Abubakar Mahmoud Gumi — 528
53:45 Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.
53:46 Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.
53:47 Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.
53:48 Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.
53:49 Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.[1]
53:50 Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.
53:51 Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.
53:52 Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.
53:53 Da waɗanda aka birkice [1]ƙasarsu, Ya kãyar da su.
53:54 Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.
53:55 To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake [1]yin shakka?
53:56 wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.
53:57 Makusanciya[1] fa, tã yi kusa.
53:58 Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.
53:59 Shin, kuma daga wannan [1]lãbãri kuke mãmãki?
53:60 Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?
53:61 Alhãli kunã mãsu wãsã?
53:62 To, ku yi tawãli'u [1]ga Allah, kuma ku bauta (masa).
54:1 Sã'a ta yi kusa, kuma wata [1]ya tsãge.
54:2 Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"
54:3 Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.
54:4 Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.
54:5 Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.
54:6 Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.