>

Abubakar Mahmoud Gumi — 525

52:32 Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi?

52:33 Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba.

52:34 Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne.

52:35 Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta?

52:36 Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba.

52:37 Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya?

52:38 Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne.

52:39 Shin, Yanã da[1] 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne?

52:40 Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar?

52:41 Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa?

52:42 Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi.

52:43 Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki!

52:44 Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna.

52:45 To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa.

52:46 Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su.

52:47 Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba.

52:48 Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnun Mu, kuma ka tsarkake[1] Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu).

52:49 Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) da lõkacin jũyãwar taurãri.