Abubakar Mahmoud Gumi — 523
51:52 Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci."
51:53 shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.
51:54 Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.
51:55 Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.
51:56 Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.
51:57 Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.[1]
51:58 Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.
51:59 To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.
51:60 Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.
52:1 Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã).
52:2 Da wani littãfi rubũtacce.
52:3 A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa.
52:4 Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda).
52:5 Da rufin nan da aka ɗaukaka.
52:6 Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa).
52:7 Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.
52:8 Bã ta da mai tunkuɗẽwa.
52:9 Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo.
52:10 Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa.
52:11 To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
52:12 Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã.
52:13 Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa.
52:14 (A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."