>

Abubakar Mahmoud Gumi — 520

50:36 Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'?[1] (Babu).

50:37 Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).

50:38 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba.

50:39 Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi[1] game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.

50:40 Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.

50:41 Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri [1]makusanci.

50:42 Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).

50:43 Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.

50:44 Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.

50:45 Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani,[1] ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.

51:1 Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.

51:2 Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).

51:3 Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.

51:4 Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah).

51:5 Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.

51:6 Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne