Abubakar Mahmoud Gumi — 519
50:16 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar hannayẽnsa.
50:17 A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne.
50:18 Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
50:19 Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa.
50:20 Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.
50:21 Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.
50:22 (Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne."
50:23 Kuma abõkin haɗinsa[1] ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce."
50:24 (A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai."
50:25 "Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka."
50:26 "Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani."
50:27 Abõkin haɗinsa[1] ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa."
50:28 Ya ce: "Kada ku yi husũma a wur Nalhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku."
50:29 "Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyi Na."
50:30 Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe,[1] akwai wani ƙãri?"
50:31 Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
50:32 "Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa).
50:33 "Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, [1]kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali."
50:34 (A ce musu) "Ku shige ta da aminci, [1]waccan ita ce rãnar dawwama."
50:35 Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima,