>

Abubakar Mahmoud Gumi — 497

44:19 "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."

44:20 "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."

44:21 "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."

44:22 Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.

44:23 (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"

44:24 "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."

44:25 Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari.

44:26 Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.

44:27 Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.

44:28 Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.

44:29 Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka [1]a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.

44:30 Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.

44:31 Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.

44:32 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.

44:33 Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna[1]

44:34 Lalle waɗannan mutãne[1], haƙĩka, sunã cẽwa,

44:35 "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."

44:36 "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."

44:37 shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.

44:38 Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.

44:39 Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.