>

Abubakar Mahmoud Gumi — 496

44:1 Ḥ. M̃.

44:2 Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.

44:3 Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.

44:4 A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.

44:5 Umurni na daga wurin Mu. Lalle Mũ ne Muka kasance Mãsu aikãwã.

44:6 Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.

44:7 (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).

44:8 Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.

44:9 A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.

44:10 Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.

44:11 Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.

44:12 Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.

44:13 Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?

44:14 Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa[1] ne, mahaukaci."

44:15 Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).

44:16 Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.

44:17 Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.

44:18 (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."