>

Abubakar Mahmoud Gumi — 495

43:74 Lalle mãsu laifi madawwama ne a cikin azãbar Jahannama.

43:75 Bã a sauƙaƙar da ita (azãbar) daga gare su, alhãli kuwa sũ, a cikinta, mãsu kãsa magana ne.

43:76 Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sũ ne suka kasance azzãlumai.

43:77 Kuma suka yi kira, "Ya Mãliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana[1] " (Mãliku) ya ce: "Lalle kũ mazauna ne."

43:78 Lalle ne, haƙĩƙa, Mun jẽ muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku mãsu ƙi ga gaskiyar ne.

43:79 Kõ kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mũ, Mãsu tukkãwa ne.

43:80 Ko sunã zaton lalle Mũ, bã Mu jin asĩrinsu da gãnãwarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tãre da su sunã rubũtãwa.

43:81 Ka ce: "Idan har akwai ɗã ga Mai rahama, to, nĩ ne farkon mãsu bauta (wa ɗan)."

43:82 Tsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantãwa.

43:83 Sabõda haka, ka ƙyãlẽ su, su kũtsa kuma su yi wãsã har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi.

43:84 Kuma Shĩ ne wanda ke abin bautãwa a sama kuma abin bautãwa a ƙasa, kuma, Shĩ ne Mai hikima, Masani.

43:85 Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurin Sa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.

43:86 Kuma waɗanda suke kira baicin Sa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane[1] (da haka).

43:87 Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su?

43:88 Kuma da (ilmin) maganar Sa (Annabi) "Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutãne ne waɗanda bã zã su yi ĩmãni ba."

43:89 To, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, "salãmã." Sa'an nan kuma zã su sani.