Abubakar Mahmoud Gumi — 492
43:34 Kuma a gidãjensu, Mu sanya) ƙyamãre da gadãje, a kansu suke kishingiɗa.
43:35 Da zĩnãriya. Kuma dukan wancan abu bai zama ba, sai jin dãɗin rãyuwar dũniya nekawai' alhãli kuwa Lãhira, a wurin Ubangijinka, ta mãsu taƙawa ce.
43:36 Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, zã Mu lulluɓe shi da shaiɗan, watau shĩ ne abõkinsa.
43:37 Kuma lalle su haƙĩƙa sunã kange su daga hanya, kuma sunã Zaton cẽwa sũ mãsu shiryuwa ne.
43:38 Har a lõkacin da (abõkin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan) "Dã dai a tsakãnina da tsakãninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabõda haka, tir da kai ga zama abõkin mutum!"
43:39 Kuma (wannan magana) bã za ta amfãne ku ba, a yau, dõmin kun yi zãlunci, lalle ku mãsu tãrẽwa ne a cikin azãba.
43:40 Shin to, kai kanã jiyar da kurma ne, ko kanã shiryar da makãho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna?
43:41 To, kõ dai Mu tafi [1]da kai to, lalle Mũ, mãsu yin azãbarrãmu, wa ne a kansu.
43:42 Kõ kuma Mu nũna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mũ, Mãsu ĩkon tasarrufi a kansu ne.
43:43 Sabõda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kanã a kan hanya madaidaiciya.
43:44 Kuma shi (abin wahayin) ambato (na ɗaukaka) ne a gare ka da kuma ga mutãnenka, kuma zã a tambaye ku.
43:45 Kuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabãninka daga Manzannin Mu, "Shin, Mun sanya waɗansu gumãka, wasun (Allah), Mai rahama, anã bauta musu?"
43:46 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã, game da ãyõyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, sai ya ce: "Lalle nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu."
43:47 To, a lõkacin da ya jẽ musu da ãyõyin Mu, sai gã su sunã yi musu dãriya.