>

Abubakar Mahmoud Gumi — 481

41:39 Kuma akwai daga ãyõyinSa cẽwa lalle kai kanã ganin ƙasã ƙẽƙasasshiya, to, idan Mun saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura. Lalle wannan da Ya rãya ta, haƙĩƙa, Mai rãyar da matattu ne. Lalle Shĩ Mai ĩkon yi ne a kan kõwane abu.

41:40 Lalle waɗannan da ke karkacẽwa a cikin ãyõyinMu, bã su fakuwa a gare Mu. Ashe fa, wanda ake jẽfãwa a cikin Wutã ne mafĩfĩci kõ kuwa wanda zai je amintacce a Rãnar ¡iyãma? Ku aikata abin da kuke so! Lalle Shĩ Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.

41:41 Waɗannan da suka kãfirta game da Alkur'ãni a lõkacin da ya je musu, kuma lalle shi haƙĩƙa littãfi ne mabuwãyi.

41:42 ¥arna bã zã ta je masa ba daga gaba gare shi. kuma bã zã ta zo ba daga bãya gare shi. Saukarwa ce daga Mai hikima, Gõdadde.

41:43 Bã zã a fada maka ba fãce abin da aka riga aka faɗa ga Manzannin da suke a gabãninka. Lalle Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne, kuma Ma'abũcin azãba mai raɗaɗi ne.

41:44 Kuma da Mun sanya shi abin karãtu na ajamanci, lalle dã sun ce, "Don me ba a bayyana ãyõyinsa ba? Ashe, zai yiwu a sãmi littãfi ba'ajame da Manzo Balãrabe?" Ka ce: "Shi, shiriya ne da warkewa ga waɗanda suka yi ĩmãni. Kuma wadanda ba su yi ĩmãni ba akwai wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma shi wata makanta ne a kansu. Waɗannan anã kiran su daga wuri mai nĩsa."

41:45 Kuma lalle Mun bai wa Mũsã Littãfi, sai aka yi ɗãɓãni a cikinsa, Kuma ba dõmin wata kalma da tã gabata ba daga Ubangijinka, lalle dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle sũ, haƙĩƙa sunã a cikin shakka daga, gare shi, mai sanya kõkanto.

41:46 Wanda ya aikata aiki na ƙwarai to sabõda kansa ne, kuma wanda ya mũnanã, to, yanã akansa. Kuma Ubangiwinka, bã Mai zãlunci ga bãyin Sa ne ba.