>

Abubakar Mahmoud Gumi — 476

40:78 Kuma lalle haƙĩƙa, Mun aika wasu Manzanni daga gabãninka, daga cikinsu akwai wanda Muka ƙissanta maka lãbãrinsa kuma daga cikinsu akwai wanda ba Mu ƙissanta lãbãrinsa ba a gare ka. Bã ya yiwuwa ga wani Manzo ya jẽ da wata ãyar mu'ujiza fãce da iznin Allah. Sa'an nan idan umurnin Allah ya jẽ, sai a yi hukunci da gaskiya, mãsu ɓãtãwa sun yi hasara a can.

40:79 Allah ne Wanda Ya sanya muku dabbõbi dõmin ku hau daga gare su, kuma daga gare su kuke ci.

40:80 Kuma kunã da abũbuwan amfãni a cikinsu, kuma dõmin ku isar da wata buƙãta, a cikin ƙirãzanku a kansu kuma a kansu da a kan jirãge ake, ɗaukar ku.

40:81 Kuma Ya nũna muku ayõyin Sa. To, wane ãyõyin Allah kuke musu?

40:82 Ashe fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasã ba, dõmin su dũba yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafi yawa daga gare su. Kuma sun fi tsananin ƙarfi, da (yawan) gurãbun sanã'õ'i a cikin ƙasã. To, abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su ba.

40:83 A lõkacin da Manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, suka yi farin ciki da abin da ke wurinsu na ilmi[1] kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi ya wajaba a kansu.

40:84 Sa'an nan a lõkacin da suka ga azãbarMu, suka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, Shi kaɗai, kuma mun kãfirta da abin da muka kasance munã shirki da shi."

40:85 To ĩmaninsu bai kasance yanã amfaninsu ba a lõkacin da suka ga azãbarMu. Hanyar Allah wadda ta gabãta a cikin bãyin Sa. Kuma kãfirai sun yi hasãra a can.