>

Abubakar Mahmoud Gumi — 466

39:68 Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa, sai gã su tsaitsaye, sunã kallo.

39:69 Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba.

39:70 Kuma aka cika wa kõwane rai abin da ya aikata. Kuma (Allah) Shĩ ne Mafi sani game da abin da suke aikatãwa.

39:71 Kuma aka kõra waɗanda suka kãfirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a har a lõkacin da suka je mata, sai aka buɗe ƙõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Ashe, waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, sunã karanta ãyõyin Ubangijinku a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?" Suka ce, "Na'am, "kuma amma kalmar azãba ita ce ta wajaba a kan kãfirai!"

39:72 Aka ce, "Ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kaunã madawwama a cikinta. Sa'an nan mazaunin makangara yã munana."

39:73 Kuma aka kõra waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama'a-jama'a har a lõkacin da suka jẽ mata, alhãli kuwa an buɗe kõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji dãɗi, sabõda haka ku shige ta, kunã madawwama (a cikinta)."

39:74 Kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya yi mana gaskiya ga wa'adinSa, kuma Ya gãdar da mu ƙasã, munã zama a cikin Aljanna a inda muke so." To, madalla da ijãrar ma'aikata.