>

Abubakar Mahmoud Gumi — 457

38:62 Kuma suka ce: "Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai?"

38:63 "Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne?"

38:64 Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã.

38:65 Ka ce: "Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa."

38:66 "Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara."

38:67 Ka ce: "Shĩ (Alkur'ãni) babban lãbãri ne mai girma".

38:68 "Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi!"

38:69 "Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama'a (malã'iku) mafi ɗaukaka a lõkacin da suke yin husũma."

38:70 "Ba a yi mini wahayin kõme ba face cẽwa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa."

38:71 A lõkacin da Ubangijinka Ya ce wa malã'iku, "Lalle Nĩ Mai halitta mutum ne daga lãkã.

38:72 "Sa'an nan idan Nã daidaita shi, kuma Na hũra (wani abu) daga Ruhĩ Na a cikinsa to ku fãɗi kunã mãsu sujada a gare; shi."

38:73 Sai malã'ikun suka yi sujada dukansu, gabã ɗaya.

38:74 Fãce Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.

38:75 (Allah) Ya ce, "Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka ne?"

38:76 Ya ce, "Nĩ, mafifici ne daga gare shi: Kã halitta ni daga wutã, kuma Kã halitta shi daga lãkã."

38:77 Ya ce, "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai la'ananne ne."

38:78 "Kuma lalle a kanka akwai la'anaTa har zuwa rãnar sakamako."

38:79 Ya ce, "Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su."

38:80 Ya ce, "To, lalle kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri,

38:81 "Zuwa ga yinin lõkaci sananne."

38:82 Ya ce, "To, inã rantsuwa da buwãyar Ka, lalle, inã ɓatar da su gabã ɗaya.

38:83 "Fãce bãyin Ka tsarkakakku daga gare su."