Abubakar Mahmoud Gumi — 455
38:27 Kuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya. Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga wutã.
38:28 Kõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da taƙawa kamar fãjirai makarkata?
38:29 (Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni.
38:30 Kuma Muka bai wa Dãwũda Sulaimãn. Mãdalla da bãwanMu, shi. Lalle shi (Sulaimãn) mai mayar da al'amari ne ga Allah.
38:31 A lõkacin da aka gitta masa dawãki mãsu asali, [1]a lõkacin maraice.
38:32 Sai ya ce: "Lalle nĩ, na fĩfĩta son dũkiya daga tunãwar Ubangijina, har (rãnã) ta faku da shãmaki!"
38:33 "Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu[1] da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu.
38:34 Kuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini[1] Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu.
38:35 Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna.[1] Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta.
38:36 Sabõda haka Muka hõre masa iska[1] tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi, inda ya nufa.
38:37 Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin kõguna.)
38:38 Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa.
38:39 Wannan kyautar Mu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu wani bincike.
38:40 Kuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurin Mu da kyaun makõma.
38:41 Kuma ka ambaci bãwan Mu Ayyũba[1] a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba."
38:42 Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã.