Abubakar Mahmoud Gumi — 452
37:154 Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannan hukunci)?
37:155 Shin, bã ku tunãni?
37:156 Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?
37:157 To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.
37:158 Kuma suka sanya nasaba a tsakãnin Sa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"
37:159 Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.
37:160 Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
37:161 To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,
37:162 Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.
37:163 Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.
37:164 "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu,[1] fãce yanã da matsayi sananne."
37:165 "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."
37:166 "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."
37:167 Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,
37:168 "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."
37:169 "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
37:170 Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.
37:171 Kuma lalle, haƙĩƙa kalmar Mu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.
37:172 Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.
37:173 Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.
37:174 Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.
37:175 Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.[1]
37:176 Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?
37:177 To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.
37:178 Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.
37:179 Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.
37:180 Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.
37:181 Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.
37:182 Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.