Abubakar Mahmoud Gumi — 451
37:127 Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).
37:128 Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
37:129 Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.
37:130 Aminci ya tabbata ga Ilyãs.
37:131 Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
37:132 Lalle shĩ, yanã daga bãyin Mu mũminai.
37:133 Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
37:134 A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.
37:135 Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).
37:136 Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.
37:137 Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.
37:138 Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?
37:139 Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
37:140 A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.
37:141 Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.
37:142 Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
37:143 To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,
37:144 Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.
37:145 Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.
37:146 Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.
37:147 Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).
37:148 Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.
37:149 Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"
37:150 Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?
37:151 To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.
37:152 "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.
37:153 Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?