>

Abubakar Mahmoud Gumi — 450

37:103 Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago

37:104 Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!"

37:105 "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

37:106 Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.

37:107 Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.

37:108 Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.

37:109 Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.

37:110 Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

37:111 Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.

37:112 Kuma Muka yi masa bushãra[1] Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.

37:113 Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).

37:114 Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna.

37:115 Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.

37:116 Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.

37:117 Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.

37:118 Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.

37:119 Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.

37:120 Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.

37:121 Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

37:122 Lalle, sunã daga bãyin Mu mũminai.

37:123 Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

37:124 A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"

37:125 "Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"

37:126 "Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?"