Abubakar Mahmoud Gumi — 449
37:77 Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.
37:78 Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe.
37:79 Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.
37:80 Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
37:81 Lalle shi, yanã daga bãyin Mu mũminai.
37:82 Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu.
37:83 Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.
37:84 A lõkacin da ya je wa ubangijinsa da zũciya kuɓutacciya.
37:85 A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"
37:86 "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"
37:87 "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"
37:88 Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.
37:89 Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."
37:90 Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.
37:91 Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?
37:92 "Me ya sãme ku, bã ku magana?"
37:93 Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.
37:94 Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.
37:95 Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,
37:96 "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"
37:97 Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."
37:98 Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.
37:99 Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."
37:100 "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."
37:101 Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro [1]mai haƙuri.
37:102 To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."