>

Abubakar Mahmoud Gumi — 448

37:52 Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"

37:53 "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"

37:54 (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"

37:55 Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.

37:56 Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."

37:57 "Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."

37:58 "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."

37:59 "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"

37:60 Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.

37:61 Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.

37:62 Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?

37:63 Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.

37:64 Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.

37:65 Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.

37:66 To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.

37:67 Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.

37:68 Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.

37:69 Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.

37:70 Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.

37:71 Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.

37:72 Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.

37:73 Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.

37:74 Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

37:75 Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.

37:76 Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.