Abubakar Mahmoud Gumi — 447
37:25 Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?
37:26 Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.
37:27 Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.
37:28 Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."
37:29 Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba.
37:30 "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."
37:31 "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."
37:32 "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."
37:33 To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.
37:34 Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.
37:35 Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.
37:36 Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?
37:37 Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.
37:38 Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.
37:39 Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
37:40 Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
37:41 Waɗannan sunã da abinci sananne.
37:42 Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.
37:43 A cikin gidãjen Aljannar ni'ima.
37:44 A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.
37:45 Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.
37:46 Farã mai dãɗi ga mashãyan.
37:47 A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,
37:48 Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.
37:49 Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.
37:50 Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.
37:51 Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."